Sinopsis
A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.
Episodios
-
Dr Yahuza Getso kan sabbin hare-hare ƴan bindiga a Arewacin Najeriya
20/11/2025 Duración: 03minMatsalolin tsaro na ci gaba da ɗaukar sabon salo a Tarayyar Najeriya, bayan da a baya-bayan nan aka ga yadda ƴan bindiga a yankin arewa maso yammacin ƙasar suka sace ɗalibai aƙalla 25 a jihar Kebbi, yayinda ana tsaka da jimamin wannan kuma aka sake ganin yadda suka kai hari wata majami’ar jihar Kwara tare da kashe mutane 2 da kuma sace wasu da dama. Wannan na zuwa ne kwanaki bayan dakarun Sojin Najeriyar sun sanar da samun gagarumar nasara a kan ƴan ta’adda musamman bayan barazanar Trump ta ɗaukar matakin Soji kan ƙasar ta yammacin Afrika. Dangane da wannan Nura Ado Suleiman ya tattauna da masanin tsaro a Najeriyar Dr Yahuza Getso........
-
Kanal Muhammad Sani Makiga kan yadda matsalar tsaro ke komawa ɗanya a arewacin Najeriya
19/11/2025 Duración: 03minGwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum ya buƙaci rundunonin sojin Najeriya na sama da na ƙasa da kuma na ruwa, da su ƙaddamar da gagarumin farmaki kan sansanonin ƴan ta’addan da ke zagayen Yankin Tafkin Chadi, domin murƙushe matsalar tsaron da ta addabi Yankin. Kiran da gwamnan na Borno ya yi a farkon makon nan, na zuwa ne a yayin da matsalolin tsaro ke sake ta’azzara a sassan arewacin ƙasar, ciki har da satar ɗaliban da aka yi jihar Kebbi. Domin jin yadda masana tsaro ke kallon wannan lamari Nura Ado Suleiman ya tattauna da Kanal Muhammad Sani Ibrahim Makiga mai ritaya, masanin tsaro a Najeriya.
-
Hon Sani Ahmad Toro kan yadda Najeriya ta gaza samun tikitin World Cup
18/11/2025 Duración: 03minFatan Najeriya na samun gurbi a gasar cin kofin duniyar da za'a yi a shekara mai zuwa ya gushe, sakamakon rashin nasarar da ƙungiyar Super Eagles ta yi a hannun ƙasar Congo. Wannan shi ne karo na biyu a jere da Najeriya ba zata je gasar ta dunitya ba, bayan gaza zuwa Qatar shekaru 4 da suka gabata, kafin wannan karo. Bashir Ibrahim Idris, ya tattauna da tsohon sakatare janar na Hukumar Kwallon Kafa Najeriya, Hon Sani Ahmad Toro game da wannan koma baya, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana a kai.
-
Sanata Bala Mohammad kan zaɓen sabbin shugabannin jam'iyar PDP a matakin ƙasa
17/11/2025 Duración: 03minBabbar jam'iyyar adawa a Najeriya, PDP ta gudanar da babban taronta na ƙasa a birnin Ibadan na jihar Oyo da ke yankin Kudu maso yammacin ƙasar, inda ta zaɓi sabbin shugabanninta a matakin ƙasa. Jam’iyyar ta ɗauki tsauraran matakai yayin taron mai cike da cece-kuce, ciki harda korar wasu manyan jiga-jiganta da suka haɗa da ministan Abuja Nyesom Wike da wasu ƙarin mutum 10. A tataunawarsa da Ahmad Abba, gwamnan jihar Bauchi kuma shugaban gwamnonin PDP, Sanata Abdulkadir Bala Mohammad, ya ce umurnin kotu suka bi wajen gudanar da wannan taro kuma sun samu nasara. Ku latsa alamar sauti don sauraron zantawar tasu............
-
Hon Hamisu Mu'azu Shira kan dambarwar da ke tattare da babban taron jam'iyyar PDP
14/11/2025 Duración: 03minShugaban kwamitin shirya babban taron Jam'iyyar PDP na ƙasa a birnin Ibadan dake Najeriya, Umar Fintiri, wanda shi ne Gwamnan Adamawa, ya ce babu abinda zai hana su gudanar da taron da suka shirya gobe asabar. Fintiri ya bayyana haka ne bayan wani gagarumin taron da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar da suka gudanar yau a birnin Abuja. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Hon Hamisu Mu’azu Shira, ɗaya daga cikin jiga jigan jam’iyyar, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana a kai.
-
Dr Harbau kan asarar kasuwar hannayen jarin Najeriya mafi muni a shekaru 10
13/11/2025 Duración: 03minKasuwar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya ta tafka hasarar Naira Tiriliyan 4 da Biliyan 600 a ranar Talata, sakamakon matakin da masu linƙaya cikin kasuwar suka ɗauka na sayar da hannayen jarinsu cikin gaggawa saboda dalilai da dama ciki har da tsoron faɗuwa. Hasarar ta fiye da Naira Tiriliyan 4, ita ce mafi muni da kasuwar hannayen jarin Najeriyar ta fuskanta cikin shekaru 10. Domin jin dalilan da suka janyo aukuwar hakan da sauran lamura masu alaƙa, Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Aminu Idris Harbau masanin tattalin arziƙi a Najeriya. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar...
-
Ba mu taɓa bai wa wani ɗan ta’adda ko anini ba – Malam Uba Sani
12/11/2025 Duración: 03minDai dai lokacin da wasu jita-jita ke nuna cewa mahukuntan Najeriya kan biya kuɗaɗen fansa ga ƴan bindiga gabanin kuɓutar da ɗimbin mutanen da suke garkuwa dasu, ko kuma ga waɗanda suka aje makamansu a jihohin arewa maso yammacin ƙasar, Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya yi iƙirarin cewa bai taɓa biyan ko sisin kwabo ga ƴan bindiga ba. Ku latsa alamar sauti don sauraron tattaunawar Gwamna Uba Sani da Khamis Saleh................
-
Abubakar Ibrahim kan taron sauyin yanayi na COP30 da ke gudana a Brazil
11/11/2025 Duración: 03minAn bude traon Majalisar Dinkin Duniya a kan sauyin yanayi da ake kira COP 30 a Brazil inda masana muhalli da sauyin yanayi daga kasashen duniya da kuma kungiyoyin kare muhallin ke halarta a kasar Brazil. Za'a kwashe makwanni biyu ana gudanar da wannan taro wanda zai mayar da hankali a kan ci gaba ko akasin haka da aka samu a kan wannan matsala. Dakta Abubakar Ibrahim, Malami kuma mai bincike a Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria ya yi tsokaci a kan matsalar musamman ganin irin illar da take yi a yankin arewacin Najeriya. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakkiyar tattaunawarsa da Bashir Ibrahim Idris.
-
Gwamnatin Yobe za ta gina sabon asibitin ƙoda a Gashua inda cutar tafi ƙamari
10/11/2025 Duración: 03minGwamnatin Jihar Yobe dake Najeriya tace za ta ƙara gina manya asibitoci a kananan Hukumomi 3 wadda suka hada da Gashua, Potiskum da kuma Nguru, baya ga gina wani wannan sabon asibitin kula da masu fama da cutar ƙoda a Garin Gashua inda cutar tafi ƙamari a jihar. Haka kuma gwamnatin ta ce zata gina wasu makarantu na musamman a kowacce mazaɓa 178 da ake da su a jihar domin ƙara inganta karatun tun daga tushe. Gwamna Jihar, Mai Mala Buni ne ya bayyana haka a tattaunawarsa da wakilinmu Bilyaminu Yusuf. Latsa alamar sauti don jin tattaunawarsu....
-
Barr Abdullahi Jalo kan ƙoƙarin warware barazanar Trump na kai hari Najeriya
06/11/2025 Duración: 03minYayin da ake ci gaba da lalubo hanyar warware matsalar barazanar Donald Trump na kai hari Najeriya, wasu masana na bayyana cewar ta hanyar diflomasiya kawai za a iya warware wannan dambarwa. Barr Abdullahi Ibrahim Jalo na ɗaya daga cikin su. Ku latsa alamar sauti don sauraron yadda tattaunawar su da Bashir Ibrahim Idris ta gudana..............
-
Shu'aibu Mikati akan tasirin barazanar Trump ga tattali arzikin Najeriya
05/11/2025 Duración: 03minBarazanar Shugaban Amurka Donald Trump kan Najeriya na ci gaba da janyo cecekuce a ƙasar da kuma ƙetare, kuma tuni wannan batu ya fara tasiri a musamman kan tattalin arzikin ƙasar. Faduwar hannayen jarin Najeriya da aka gani a wannan mako, ta janyo hankalin mutane yayin da ake ganin kai tsaye yana da alaƙa da barzanar ta Trump. Rukayya Abba Kabara ta tattauna da kwararre kan harkokin tattalin arziki a Najeriya, Alhaji Shu’aibu Mikati kan wannan batu, ga kuma yadda tattaunawar tasu ta kasance.
-
Ambasada Abubakar Cika kan barazanar kai wa Najeriya hari da Amurka ta yi
04/11/2025 Duración: 03minYayin da hukumomin Najeriya suka yi watsi da barazanar shugaban Amurka na kai wa ƙasar hari saboda zargin kashe Kiristoci, ƴan kasar da dama na ci gaba da bayyana ra'ayi a kan matsayin na shugaba Donald Trump. Daga cikin waɗanda suka bayyana ra'ayin su a kan wannan barazana har da tsohon Jakadan Najeriya a ƙasar Iran, Ambasada Abubakar Cika, kamar yadda za ku ji a tattaunawarsu da Bashir Ibrahim Idris.
-
Tattaunawa da Alhaji Shehu Ashaka kan matsalolin tsaro a arewacin Najeriya
03/11/2025 Duración: 03minA Najeriya, babban abin da ya fi ci wa al’ummar yankin Arewacin ƙasar tuwo a ƙwarya ita ce matsalar rashin tsaro, inda hare-haren ƴanbindiga ke ci gaba da haddasa asarar rayukan jama’a, da gurgunta harkar noma da kuma kasuwanci a yankin baki-ɗayansa. Dangane da haka ne Bashir Ibrahim Idris ya zanta da ɗaya daga cikin dattawan yankin Alhaji Shehu Ashaka, ga kuma yadda zantawarsu ta kasance. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.
-
Ambasada Muhammad Sani kan rikicin zaɓen Kamaru
31/10/2025 Duración: 03minHar yanzu ana ci gaba da zaman ɗar-ɗar a ƙasar Kamaru sakamakon tashin hankalin da ya biyo bayan zaɓen shugaban ƙasar da aka bayyana shugaba Paul Biya a matsayin wanda ya samu nasara. Shugaban 'yan adawa Issa Tchiroma Bakary da ya zo na biyu ya ƙi amincewa da sakamakon, inda ya buƙaci jama'a da su sake fitowa zanga zanga a ranakun litinin da Talata da kuma Laraba na makon gobe, yayin da a ɓangare ɗaya gwamnati ke barazanar ladabtar da duk wanda ya saɓa dokokin ƙasar, ciki harda shi Isa Tchiroma. Domin tattauna halin da ake ciki a ƙasar, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da tsohon Jakadan Kamaru a Faransa, Ambasada Muhammadu Sani. Ku alatsa alamar sauti don sauraren tattaunawarsu...
-
Fatima Nzi Hassan kan ta'azzarar sauyin yanayi, yayin da ake gab da fara taron COP30
30/10/2025 Duración: 03minYayin da ake shirin fara taron sauyin yanayi na duniya da ake kira COP30 a Brazil, a ranar 10 ga watan gobe, ƙungiyar OXFAM ta fitar da sanarwa inda take sake bayyana damuwa a kan rashin ɗaukar kwararan matakai wajen aiwatar da yarjejeniyar da aka ƙulla shekaru 10 da suka gabata a birnin Paris. Game da wannan Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da darakatar ƙungiyar ta OXFAM a Nahiyar Afrika Malama Fatima Nzi Hassan. Danna alamar saurare domin jin cikakkiyar tattaunawar.
-
Dr. Abdulhakim Garba Funtuwa kan dambarwar yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza
29/10/2025 Duración: 03minGa alama yajejeniyar tsagaita wutar da Isra'ila ta ƙulla tsakaninta da Hamas, wadda Amurka ta tsara ta kama hanyar rugujewa, sakamakon umarnin da Firaminista Benjamin netanyahu ya bayar na ƙaddamar da sabbin hare-hare a Gaza. Wannan ya biyo bayan abinda ya kira ƙin bada gawarwakin sauran Yahudawan da Hamas ta yi garkuwa da su. Domin tattauna wannan dambarwa, Bashir Ibrahim Idris, ya tuntuɓi Dakta Abdulhakin Garba Funtua, mai sharhi a kan harkokin Gabas ta Tsakiya, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.........................
-
Tattaunawa da Muhammad Sani Makigal kan garambawul ɗin Tinubu a ɓangaren tsaro
28/10/2025 Duración: 03minA baya-bayan nan ne, gwamnatin Najeriya ta gudanar wani garambawul ga sha’anin tsaron ƙasar, ciki kuwa har da matakin da shugaba Bola Tinubu ya yi na sauya kusan ilahirin manyan hafsoshin tsaron ƙasar, lamarin da ya janyo cece-kuce. Ra’ayoyi sun mabanbanta game da wannan mataki na garambawul ga ɓangaren na tsaro a Najeriya, inda wasu ke ganin batu ne da ya dace lura da yadda matsalolin tsaro ke ci gaba da ta’azzara, yayinda wasu ke alaƙanta batun da siyasa. A gefe guda, Najeriyar ta gamu da jita-jitar yunƙurin juyin mulki, wanda kuma kwanaki bayan tsanantar jita-jitar shugaban ya gudanar da wannan garambawul, Dangane da hakan ne kuma Michael Kuduson ya tattaunawa da masanin tsaro a ƙasar Muhammad Sani Makigal. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar....
-
Tattaunawa da Fatima Dangote kan shirin faɗaɗa aikin matatar Ɗangote
27/10/2025 Duración: 03minKatafaren kamfanin Dangote, ya sanar da shirin faɗaɗa matatar sa mai samar da tacaccen gangar mai 650,000 zuwa miliyan guda da 400,000 a kowacce rana. Shugaban rukunin kamfanin Dangote Alhaji Aliko Dangote ya ce za'a kwashe shekaru uku ana aikin faɗaɗa matatar wadda ya ce za ta zama mafi girma a duniya. Dangane da wannan ci gaba ne kuma Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da babbar manajar rukunonin kamfanin, Fatima Aliko Dangote. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar hirar.....
-
Usman Ture kan zaɓen shugaban ƙasar Cote d'Ivoire na gobe Asabar
24/10/2025 Duración: 03minA Cote d’Ivoire, a jajiberin zaɓen shugaban ƙasar, hukumomi sun ɗauki matakan da suka dace na ganin an gudanar da zaɓen ba tare da an fuskanci wata matsala ba. To domin jin ko a ina aka kwana ,Abdoulaye Issa ya tattauna da Usman Ture,wani ɗan ƙasar ta Cote d’ivoire da ya karɓi katinsa na zaɓe. Latsa alamar sauti domin jin yadda tattaunawarsu ta gudana...
-
Dr Isa Abdullahi kan tasirin ƙananan bankunan a Najeriya
23/10/2025 Duración: 03minSannu a hankali ƙananan bankuna na bada gagarumar gudumawa wajen ci gaban tattalin arzikin Najeriya, la'akari da yadda jama'a ke komawa hada hada da su maimakon manyan bankunan da aka sani a baya. Ko a jiya Moniepoint ya sanar da samun jarin Dala miliyan 200 domin inganta harkokin sa. Domin sanin tasirin wadannan ƙananan bankunan, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin tattalin arziki, Dr Isa Abdullahi na Jami'ar Kashere. Ku latsa alamar sauti don jin yadda zantawarsu ta gudana..................