Bakonmu A Yau

Kanal Muhammad Sani Makiga kan yadda matsalar tsaro ke komawa ɗanya a arewacin Najeriya

Informações:

Sinopsis

Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum ya buƙaci rundunonin sojin Najeriya na sama da na ƙasa da kuma na ruwa, da su ƙaddamar da gagarumin farmaki kan sansanonin ƴan ta’addan da ke zagayen Yankin Tafkin Chadi, domin murƙushe matsalar tsaron da ta addabi Yankin. Kiran da gwamnan na Borno ya yi a farkon makon nan, na zuwa ne a yayin da matsalolin tsaro ke sake ta’azzara a sassan arewacin ƙasar, ciki har da satar ɗaliban da aka yi jihar Kebbi. Domin jin yadda masana tsaro ke kallon wannan lamari Nura Ado Suleiman ya tattauna da Kanal Muhammad Sani Ibrahim Makiga mai ritaya, masanin tsaro a Najeriya.