Sinopsis
A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban daban domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya. wani lokacin kuma wasu manyan jami'an gwamnati da masu fada aji sukan kawo muna ziyara domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin da suka shafe su ko kuma ci gaban kasa.
Episodios
-
Sunusi Bature game da taron baje-kolin kafafen yaɗa labarai na-afrika karo na 14
22/10/2025 Duración: 02minAn buɗe taron baje kolin kafafen yaɗa labarai na Afrika da ake kira AFRICAST karo 14 a birnin Lagos da ke Najeriya, inda masu ruwa da tsaki a harkar yaɗa labarai daga nahiyar da kuma sassan duniya ke halarta.Domin ƙara inganta ayyukan yaɗa labarai, wasu daga cikin mahalarta wannan taro na ganin cewa ya zama wajibi a samar da dokokin da za su sa-ido kan ayyukan kafafen sada zumunta da kuma sauran hanyoyin yaɗa labarai ta yanar gizo. Sanusi Bature Dawakin Tofa, shi ne mai magana da yawun gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Yusuf, kuma wanda ya wakilce shi a taron, a zantawarsa da Abdoulkarim Ibrahim Shikal, ya ce lalle akwai buƙatar samar da gyara a wannan fanni. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar...................
-
Gwamna Dikko Raɗɗa kan shirin bunƙasa lantarki a jihohin Kano da Jigawa da Katsina
21/10/2025 Duración: 03minGwamnatocin jihohin Katsina da Kano da kuma Jigawa da ke arewa maso yammacin Najeriya sun kulla haɗakar inganta wutar lantarkin ga jihohin uku. Gwamnonin Kano, Jiagwa da Katsina sun shiga yarjejeniyar haɗin gwiwa kan bunƙasa wutar lantarki a jihohin uku da ke arawacin Najeriya, tare da zuba hannun jari a kamfanonin Future Energies Africa (FEA) da na rarraba wutar lantarki a jihohin uku wato KEDCO. Hakan ya fito fili ne bayan wani taro da gwamnonin jihohin uku da suka hada da Malam Umar Dikko Radda da Abba Kabir Yusuf da kuma Umar Namadi suka gudanar a ƙasar Morocco inda suka tattauna da kamfanin Future Energies Africa da Kedco da sauran masu ruwa da tsaki a harkar makamashi. A zantawarsa da RFI Hausa, Gwamnan jihar Katsina Malama Dikko Rada ya ce suna son fito da haryar yin haɗaka a fannin wutar lantarki tsakanin jihohin makwabtan juna ta hanyar zuba jari naira biliyan 50 domin samar da wutar da yankin ke bukata. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar................
-
Birgediya Tukur Gusau akan jita-jitar yunƙurin juyin mulki a Najeriya
20/10/2025 Duración: 03minBabbar Cibiyar rundinonin sojin Najeriya ta yi watsi da rahotannin dake cewa an yi yunkurin juyin mulkin a kasar, abinda ya kai ga kama wasu hafsoshi guda 16. Daraktan yada labaran Cibiyar janar Tukur Gusau ya shaidawa Bashir Ibrahim Idris a zantawarsu cewar, sojojin da aka kama ana tuhumar su ne da laifin saba dokoki na soji amma ba juyin mulki ba. Ga yadda zantawarsu ta gudana.
-
Tattaunawa da Isah Sunusi kan horon da Amnesty ta baiwa matasa a Najeriya
17/10/2025 Duración: 03minƘungiyar Amnesty International a Najeriya ta shirya wani taro a Lagos domin horar da matasa a kan yadda za su kare haƙƙoƙin jama'a a yankunan da suka fito.Taron wanda zai gudana a shiyoyin Najeriya guda 6 ya ƙunshi matasa daga shiyar kudu maso yammacin kasar. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Daraktan ƙungiyar a Najeriya, Malam Isa Sanusi. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakkiyar tattaunawar.............