Bakonmu A Yau

Sanata Bala Mohammad kan zaɓen sabbin shugabannin jam'iyar PDP a matakin ƙasa

Informações:

Sinopsis

Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, PDP ta gudanar da babban taronta na ƙasa a birnin Ibadan na jihar Oyo da ke yankin Kudu maso yammacin ƙasar, inda ta zaɓi sabbin shugabanninta a matakin ƙasa. Jam’iyyar ta ɗauki tsauraran matakai yayin taron mai cike da cece-kuce, ciki harda korar wasu manyan jiga-jiganta da suka haɗa da ministan Abuja Nyesom Wike da wasu ƙarin mutum 10. A tataunawarsa da Ahmad Abba, gwamnan jihar Bauchi kuma shugaban gwamnonin PDP, Sanata Abdulkadir Bala Mohammad, ya ce umurnin kotu suka bi wajen gudanar da wannan taro kuma sun samu nasara. Ku latsa alamar sauti don sauraron zantawar tasu............