Ilimi Hasken Rayuwa

Har yanzu Malama tsangaya na amfani da Ajami wajen musayar sakonni

Informações:

Sinopsis

Shirin a wannan mako, kareshe ne kan maudu’in da muka tattaunawa a makonni biyun da suka gabata, wanda ya mayar da hankali kan yadda rubutun Ajami a kasar Hausa ya yi shura, da kuma yadda yake neman bacewa a wannan zamani. Yayin da ake ganin har yanzu a Jamhuriyar Nijar, akwai yankunan da suke amfani da ajami wajen isar da sakonni, Malaman tsangaya daga Najeriya ma suna amfani da wannan tsarin rubutu wajen musayar bayanai a tsakaninsu. Yaɗuwar addinin Islama a Ƙasar Hausa masana suka ce, ya taimaka sosai wajen shaharar wannan salo na rubutu, sannan kuma ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen inganta hanyoyin sadarwa na wancan lokaci. A tattaunawarmu da masanin tarihi daga Kanon Najeriya, farfesa Tijjani Naniya, ya bayyana cewa, zuwan turawan mulkin mallaka, shine musabbabin gushewar wannan rubutu a kasar Hausa, amma a wancan lokaci, rubutun na ajami ya ci kasuwa tsakanin masana, malamai, sarakuna da kuma ‘yan kasuwa.