Kasuwanci

Masana a kan cire Najeriya daga jerin ƙasashen da ke ɗaukar nauyin ta’addanci

Informações:

Sinopsis

Shirin a wannan makon ya yi dubi ne kan zare sunan Najeriya da cibiyar da ke sanya idanu kan almundahanar kuɗaɗe da ɗaukar nauyin ta’addanci a duniya ta yi cikin baƙin kundinta.  A makon da ya gabata ne, Cibiyar nan ta Yaƙi da Masu Safarar Kuɗi da Ɗaukar Nauyin Ta’addanci ta duniya (FATF), ta sanar da cire sunan Najeriya daga jerin ƙasashen da take ɗaukarsu a matsayin masu wanan ɗabi’a. Wannan mataki ba iya Najeriya ta shafa ba, harma da ƙasashen Burkina Faso da Afrika ta Kudu da ma Mozambique duk a nahiyar Afrika. Cibiyar wadda ke da hedikwata a birnin Paris na ƙasar Faransa, wadda ke gudanar da binciken kwakwaf kan yadda ake hada-hadar kuɗaɗe tsakananin ma’aikatun gwamnati da hukumomi ko kuma cibiyoyin gwamnati ta ce duk da cire waɗannan ƙasahe cikin baƙin littafinta, har yanzu za’a ci gaba da sanya idanu akan waɗannan ƙasashe. Latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba................