Wasanni
Adawar magoya bayan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na ƙarawa gasar armashi
- Autor: Vários
- Narrador: Vários
- Editor: Podcast
- Duración: 0:10:00
- Mas informaciones
Informações:
Sinopsis
Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan mako ya yi duba ne kan yadda adawar magoya bayan ƙungiyoyi ke karawa kwallon ƙafa tagomashi. Wasanni da dama ne dai ke samu karbuwa a duniya da suka haɗa da kwallon ƙafa da kwallon kwando da kwallon Cricket da Tennis da dai sauransu, amma kuma kowane wasa na da irin nashi magoya baya da suke matuƙar ƙaunarsa da so a duniya. Bincike ya nuna cewa babu wani wasa da ta fi kwallon kafa magoya baya a duniya, inda aƙalla mutane biliyan 3 da rabi ne ke sha'awar wasan baya ga ƴan kwallon kansu da suka kai miliyan 250, waɗanda hukumomin kwallon ƙafa a duniya FIFA ta yiwa rijista. Hatta a Najeriya nuna sha'awa na magoya baya ba ya misaltuwa, domin babu lungu da sako da wasan bai samu karɓuwa ba musamman ma wasannin nahiyar Turai da ya fi can hankali. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.