Bakonmu A Yau
Dr. Kabir Adamu kan kiran da Janar Christopher ya yi na gine iyakokin Najeriya
- Autor: Vários
- Narrador: Vários
- Editor: Podcast
- Duración: 0:06:39
- Mas informaciones
Informações:
Sinopsis
Babban hafsan tsaron sojin Najeriya Janar Christopher Musa, ya yi kira da a gina katanga a ɗaukacin iyakokin ƙasar domin kawo karshen matsalolin tsaro da ƙasar ke fuskanta. Janar Musa ya bayyana hakan ne yayin wani taro kan tsaro da aka gudanar a Abuja babban birnin ƙasar, inda ya bayyana katange iyakokin ƙasar a matsayin mai matuƙar muhimmanci, yana mai misali da yadda ƙasashen Pakistan da Saudiya suka katange iyakokinsu da Afghanistan da Iraq a matsayin abin koyi. Ku latsa alamar sauti don sauraron zantawar Ahmad Abba da Dr. Kabir Adamu, shugaban kamfanin tsaro na Beacon Security and Intelegence a Najeriya........