Sinopsis
Shirin Lafiya yana tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jamaa, Sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Talata da yamma.
Episodios
-
Lafiya Jari Ce: Illar rashin zuwa awon ciki ga lafiyar mata da jariransu
10/02/2025 Duración: 10minShirin ''Lafiya Jari ce'' tare da Azima Bashir Aminu a wannan mako ya yi duba ne kan matsalar rashin zuwa awo da ke matsayin babban ƙalubalen ga mata masu juna biyu a yayin goyon ciki ko kuma haihuwa, matsalar da aka fi ganin ta’azzararta a yankunan karkara, wadda a lokuta da dama ke kaiwa ga asarar rayukan walau uwa ko jariri. Ƙorafe-ƙorafen jami’an lafiya na ci gaba da yawaita kan matsalolin da suka dabaibaye tsarin renon ciki da kuma haihuwa a yankunan karkara, matsalar da wala’alla ake ganin ta na da alaƙa ta ƙut da ƙut da halin matsi ko kuma tsadar rayuwar da ake fama da ita wadda ta ƙai ƙololuwa a yankin arewacin Najeriya mai fama da durƙushewar ɓangaren kiwon lafiya.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.
-
Barazanar da fannin lafiya ke fuskanta kan ficewar likitoci daga Najeriya
27/01/2025 Duración: 10minShirin lafiya Jari ce na wannan makon ya taɓo batun yadda kwararrun likitoci ke tserewa daga Najeriya, inda wasu alkaluma suka nuna cewa a cikin shekaru biyar da suka gabata, sama da likitoci dubu 16 suka fice daga ƙasar don yin aiki a wasu ƙasashen ketare, lamarin da ke barazana ga tsarin kula da lafiya a ƙasar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu............
-
Ƙoƙarin da ƙungiyoyi ke yi don magance cutar yanar ido tsakanin al'ummar Nijar
20/01/2025 Duración: 10minShirin Lafiya jari ce bisa al'ada tare da Azima Bashir Aminu na yin duba ne kan wasu batutuwa da suka shafi kiwon lafiya, kuma a wannan makon ya yada zango a Jamhuriyyar Nijar inda wasu ƙungiyoyin agaji suka yiwa tarin mutanen da ke fama da matsalar cutar yanar ido aiki a ƙokarin dawo musu da ganinsu. A cikin shirin za ku ji yadda kusan kashi 2 cikin 100 na al'ummar wannan ƙasa ta yankin Sahel ke fama da matsalar lalurar ta yanar ido a wani yanayi da mahukunta tare da taimakon ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa ke fatan magance matsalar zuwa ƙasa da kashi 1 nan yan shekaru masu zuwa.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
-
Tsarin tazarar Iyali ya fara samun karɓuwa a yankunan karkara
06/01/2025 Duración: 09minShirin lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu bisa al’ada kan taɓo batutuwan da suka shafi kiwon lafiya ko kuma a lokuta da dama ya lalubo ƙalubalen da fannin lafiyar ke fuskanta don ankarar da mahukunta da nufin ɗaukar matakan gyara. A wannan makon shirin na Lafiya Jari ce ya mayar da hankali kan tazara ko kuma tsarin iyali ko Family Planning wanda ke sahun shawarwarin kiwon lafiya da ke ganin kakkausar suka musamman a arewacin Najeriya wala’alla saboda yadda tsarin ya ci karo da al’adun al’ummomin wannan yanki, sai dai a baya-bayan nan alamu na nuna yadda wannan tsari ke samun karɓuwa gadan-gadan.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin....