Sinopsis
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.
Episodios
-
Sharhi kan kyautar gwarzon ɗan wasan Afrika da Ademola Lookman ya lashe
23/12/2024 Duración: 09minShirin Duniyar Wassani a wannan makon ya yi duba ne game da kyautar gwarzon ɗan wasan Afrika da aka bayar. A ranar Litinin din da ta gabata ne dai Hukumar da ke kula da kwallon ƙafar nahiyar Afrika wato CAF, ta bayar da kyautar gwarzon nahiyar Afrika wanda yafi bajinta a wannan shekarar da muke bankwana da ita. Ɗan wasan gaba na tawagar Super Eagles ta Najeriya Ademola Lookman ne ya samu nasarar lashe wannan kyauta, biyo bayan irin bajintar da ya nuna ga ƙasar da kuma ƙungiyarsa ta Atlanta. Samun nasarar lashe wannan kyauta da ɗan wasan yayi dai ta sanya zamowa cikin jerin ƴan wasa 6 na Najeriya da a tarihi suka taɓa lashe ta.Ku latsa alamar sauti don jin cikakken shirin tare da Khamis Saleh........
-
Sauye-sauyen da aka samu a bana a gasar wasan kokuwar gargajiya ta Nijar
16/12/2024 Duración: 10minShirin Duniyar Wasanni a wannan makon, yayi duba ne game da gasar kokuwar gargajiya a Jamhuriyar Nijar, wacce za a faro a ranar 20 ga wannan wata na Disamba nan a jihar Dosso da ke rike da takobi ko kambun gasar, inda ƴan wasa 80 daga Jihohi 8 na Nijar za su fafata har zuwa 29 ga watan, don samun sabon sarkin ƴan kokuwa wanda ke lashe kyautar takobi da kuɗaɗe da sauran kyautuka. Sai dai wani hanzari da ba gudu ba shi ne yadda a bana aka samu wasu sabbin sauye-sauye musamman ɓangaren dokokin wannan gasa.Ku latsa alamar sauti don sauraren shirin tare da Khamis Saleh..........
-
Ƴan wasan lik ɗin Najeriya na fuskantar barazana sakamakon tafiye tafiye ta mota
09/12/2024 Duración: 09minShirin Duniyar Wasanni a wannan makon ya yi duba ne kan yadda ƴan wasa a Lik din Najeriya ke fuskantar barazana a tafiye tafiye ta mota da suke yi don yin wasa. Yin amfani da motoci wajen jigilar ƴan wasan da ake fafatawa a gasar Lik ɗin Najeriya ba sabon abu bane, ganin yadda mafi yawancin ƙungiyoyin da ke fafatawa a wannan gasa sun fi amfani da motoci wajen kai ƴan wasansu jihohin ko garuruwan da za su fafata wasa. Irin waɗan nan tafiye tafiye dai na haifar da barazana ga rayuwar ƴan wasan musamman idan aka yi la’akari da rashin ƙyaun hanyoyi ko kuma da kuma matsalar tsaro.Ƙungiyar El-Kenemi Warriors ce ta baya-bayan nan da ƴan wasanta suka fuskanci wannan barazana, a hanyar su ta koma birnin Maiduguri bayan buga wasan mako na 14 da suka yi Ikorodu City a birnin Lagos.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh......
-
Najeriya ce zakara a wasannin sojoji na Afrika karo na biyu da aka gudanar
02/12/2024 Duración: 09minShirin Duniyar Wasanni na wannan mako yayi duba ne kan yadda aka kammala wasanni sojoji na nahiyar Afrika. Wannan ne dai karo na biyu da tawogogin ƙasashe 20 suka fafata a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, inda kuma tawagar ƴan wasan sojoji ta Najeriya ta zamo zakara, bayan da ta samu nasarar lashe lambar zinari 114 da azurfa 65 sai kuma tagulla 55 a jumlace ke nan ta samu lambobin yabo 234. Ƙasar Aljeriya ke bi mata a matsayin na 2 da lambar zinari 53 da azurfa 22 sai kuma agulla 21, a jumlace ita kuma ta samu lambobin yabo 96, Kenya ce tazo ta 3 bayan da ta lashe lambobin yabo 50.Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin tare da Khamis Saleh.......