Sinopsis
Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-dabam a duniya, tare da nazari ga irin ci gaban da aka cim ma wajen binciken kimiya da fasaha da ke naman saukakawa Danadam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin irin bincike da masana ke yi domin inganta rayuwar Biladam. Shirin na zo maku ne, a duk ranar Talata a shirye-shiryenmu na safe.
Episodios
-
Yadda faɗuwar jarabar JAMB ta shafi ɗalibai da ke neman gurbin ƙaratu a Najeriya
03/06/2025 Duración: 10minShirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako ya yi duba ne kan matsalar da aka samu ta faɗuwar jarabar sharar fage ta shiga jami'o'in Najeriya JAMB, da hukumar shirya jarabawar ta ce hakan ya faru ne a sakamakon tangarɗar da aka samu ta na'ura a lokacin rubutawa. Matslar da ta hana shafi ɗalibai dubu 300 da suka rubuta jarabawar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna.........
-
Yadda Malaman makarantu suka tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a Abujan Najeriya
27/05/2025 Duración: 09minShirin na wannan mako ya ba da hankali ne kan bikin ranar yara ta duniya wanda aka saba gudanarwa a ranar 27 ga watan mayun kowacce shekara, a Najeriya yayin da ake bikin wannan rana Malaman Makarantun firamare a Abuja babban birnin ƙasar ne ke shiga watanni na uku da fara yajin aikin sai Baba ta gani, sakamakon rashin fara aiwatar da sabin tsarin mafi ƙarancin albashi na naira dubu 70 kamar yadda ƙungiyarsu ta Malaman makarantu ta bayyana. lamarin da ya ta da yajin aikin gargaɗi a baya kafin su tsunduma cikin wanda suke kai a yanzu.
-
Yadda satar amsa tsakanin dalibai ke yiwa ilimi illa musamman a Najeriya
20/05/2025 Duración: 09minShirin Ilimi Hasken rayuwa na wannan mako ya mayar da hankali kan Illonlin satar amsa tsakanin Dalibai a yayin rubuta jarabawa. Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna
-
Shirin gwamnatin Najeriya na dawo da tsarin koyarawa da harshen uwa
13/05/2025 Duración: 10minA wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan, shawarar gwamnatin tarayyar Najeriya ta dawo da tsarin amfani da harshen uwa a makarantun firamare da ke fadin kasar. Tsarin amfani da harshen uwa a makarantun firamare, wani tsari ne da aka gabatar a shekarar 2022, wadda ke da nufin inganta amfani da harsunan uwa a matsayin harshen koyarwa a makarantun firamare. Sai dai, a wancan lokaci da aka kaddamar da manufar za a yi amfani da ita ne akan Yara yan aji daya zuwa na makarantun firamare.Hakan kuwa ya biyo bayan bincike-bincike da aka gudanar wanda ya nuna cewa rashin fahimtar darusan da ake koyarwa da harshen Ingilishi ya bada gudunmowa wajen barin Yara makaranta da kuma haifar da koma-bayan ilimi a Najeriya.Sai da masana sun bayyana wasu ƙalubale da za a iya fuskanta da suka hadar da rashin wadatattun kayan koyarwa, da matsalolin zabar babban yare a cikin al'ummomi da ke amfani da harsuna da yawa.